Masari ya yi Allah wadai da hukumar Kwastam

Akwai yiwuwar kai ruwa rana tsakanin Masari da hukumar Kwastam.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari  ya yi tir da  Allah wadai da hukumar kwastan a sakamakon kashe wasu  mutane 10 da wasu jami'anta su ka yi a  lokacin da suke bin wani xan fasa qwaurin shinkafa a qaramar hukumar Jibiya dake Jihar Katsina.

Masari ya nuna fushinsa tare da gargaxin  cewar daga yanzu gwamnatin Jihar ba zata sake zuba ido tana kallon waxanda ya kamata su kare rayukan al'umma su vuge da kashe su a sakamakon tuqin ganganci .

Masari ya bayyana haka ne a  lokacin da yake miqa saqon ta'aziyyarsa da kuma jajantawa ga 'yan uwa da abokan arziqi da hatsarin ya shafa hakan yana qunshe cikin wata sanarwa da babban daraktan yaxa labaransa Abdu Labaran Malumfashi ya saka ma hannu aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta qara da cewa gwamnati na duba yiwuwar kai hukumar kwastan qara kotu don hakan ya zama darasa ga na gaba da kuma kare sake faruwar lamarin nan gaba.

A ranar 9 ga watan Ogasta,2021 wata motar jami'an kwastan ta afka cikin wasu mutane inda ta kashe mutane 10 ta kuma jikkata wasu 20 a garin Jibiya lokacin da motar kwastan xin ke bin wani xan smogal na shinkafa.

Comments