An yi ma wasu malaman makaranta jarabawar gwaji

 Zulum ya yi ma wasu malamai jarabawar gwaji

 Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya kai ziyarar bazata a wata makaranta dake garin Baga inda ya shirya ma malaman makarantar jarabawar auna fahimta.
Kakakin gwamnan Isa Gusau,ya ce an yi ma malaman jarabawar ne don a tabbatar da cancantar su da kuma kwarewar su a fagen koyo da koyarwa.
An kuma ruwaitto gwamna Zulum ya na bayyana cewar jarabawar bata nufin za'a kori wani daga cikin malaman don ya gaza, sai dai an shirya jarabawar ne don a auna fahimtar su a kuma san bangaren da ya dace a ajiye su don su hidimta ma jihar.

Comments