Posts

Masari ya yi Allah wadai da hukumar Kwastam

Image
Akwai yiwuwar kai ruwa rana tsakanin Masari da hukumar Kwastam. Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari  ya yi tir da  Allah wadai da hukumar kwastan a sakamakon kashe wasu  mutane 10 da wasu jami'anta su ka yi a  lokacin da suke bin wani xan fasa qwaurin shinkafa a qaramar hukumar Jibiya dake Jihar Katsina. Masari ya nuna fushinsa tare da gargaxin  cewar daga yanzu gwamnatin Jihar ba zata sake zuba ido tana kallon waxanda ya kamata su kare rayukan al'umma su vuge da kashe su a sakamakon tuqin ganganci . Masari ya bayyana haka ne a  lokacin da yake miqa saqon ta'aziyyarsa da kuma jajantawa ga 'yan uwa da abokan arziqi da hatsarin ya shafa hakan yana qunshe cikin wata sanarwa da babban daraktan yaxa labaransa Abdu Labaran Malumfashi ya saka ma hannu aka rabawa manema labarai. Sanarwar ta qara da cewa gwamnati na duba yiwuwar kai hukumar kwastan qara kotu don hakan ya zama darasa ga na gaba da kuma kare sake faruwar lamarin nan gaba. A ranar 9 ga...

An yi ma wasu malaman makaranta jarabawar gwaji

Image
 Zulum ya yi ma wasu malamai jarabawar gwaji  Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya kai ziyarar bazata a wata makaranta dake garin Baga inda ya shirya ma malaman makarantar jarabawar auna fahimta. Kakakin gwamnan Isa Gusau,ya ce an yi ma malaman jarabawar ne don a tabbatar da cancantar su da kuma kwarewar su a fagen koyo da koyarwa. An kuma ruwaitto gwamna Zulum ya na bayyana cewar jarabawar bata nufin za'a kori wani daga cikin malaman don ya gaza, sai dai an shirya jarabawar ne don a auna fahimtar su a kuma san bangaren da ya dace a ajiye su don su hidimta ma jihar.

e-news Hausa

Mu na sanar da ku ingantattun labarai da zarar sun fara